Old school Easter eggs.
Darus-sahaba
1jojlxKOMkX9WyteRe4hGfd...5Tlzwos6Wa8pU99NjJEjmoO7lE72qs...P8zLBUI5VEdw01bf9Bj3WN2UJZQ0kMkumqAOI9CU319yy4DVw
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka

wanna shafi yana zuwa muku kai tsaye daga masallacin jumu'a
Jami'u Abu hurairah
Dake kurna y'an kifi titin y'an smogal a karamar hukumar dala dake kano Nigeria
kar kashin jagorancin
Sheik Muhammad Sani Uthman Kurna

Home
Karatut-tukan Sheik Muhammad Thani Uthman Kurna
Mata A Musulunci
Bayanin Zakka
Bayanin Azumi
Bayanin Hajji da Umara
Kasuwanci mai ribar gaske
Muhimmin Sako Zuwa ga Ma'aurata
Tsarin Mu'amala A cikin Musulunci
Hakkokin Manzon Allah s a w Akan Alumarsa
Shin hadin kai zai yiwu tsakanin Ahalussunnah da shi a
Wadanna mata aka Haram tawa musulmi da kuma wanda aka Halarta
Hukunce - Hukunce da suka shafi mata
Jinin Al ada ga mata
Jagoran mai wa azi
Adduo in manzon Allah s a w
Falalar Karatun Al-kur'ani
Falalar Sahabbai {R.A}
Falalar Sahabbai {R.A} Daga bakin Imamai
Tarihi
Falalar Ahlulbait daga bakin Ahlussunnah
Tambayoyi masu muhimmanci A cikin Addinin Musulunci
Ayyukan Zuci
Tattaunawa Ta Nitsuwa
Addinin Shi'a
Hukunce-Hukuncen Da Suka Shafi Mata
Karatut-tukan Malamai da Lakcocin su



2014-10-12

-----------------------------------
FALALAR SAHABBAI DAGA BAKIN IMAMAI
(kashi na daya)
.
FALALAR AHLULBAITI DA MATSYINSU A WIRIN SAHABBAI DA SAURAN MUSULMI

Godiya ta tabbata ga Allah ta,ala daya hada kan sahabbai da Ahlulbaiti, suka hadu wurin Imani da yada addinin musulmi da kaunar juna da girmama juna.
Suka kuma tarbiyyanci yan baya akan haka.
.
Wannan shi ne ya sa dukkan musilmi na gaskiya yake mutukar girmama da kunar Ahlulbaiti gaba dayansu tun daga matan manzon Allah (S.A.W.) har zuwa jikokinsa zuwa tashin kiyama.
.
Kaunar Ahlulbaiti da girmama su jigo ne babba na imani. å wurin dukkan musilmi musanmman Ahlussunna.
.
A wannan gaba ba zan tsawaita ba, domin abu ne a fili ga duk mai karatu ko sauraran malamai.
Zan takaita kan maganganu ( biyu) daga ibnu taimiyya da imam Azzahabi, domin na jefi tsuntsu biyu da datse daya ,na farko bayan falalarsu, na biyu karyata zargin kin Ahlulbaiti da wasu suke tuhumar ibnu Taimiyya da almajiransa da sh.
.
Shaihul islam ibnu Taimiyya Rahimahullahu yake cewa Tabbas iyalan Manzon Allah ( S.A.W) suna da hakki akan al,umma wanda suka kebanta da shi.
Kuma sun cancanci a so su fiye da dukkan kuraishawa, Kamar yadda ya wajaba a so kuraishawa fiye da kowace kabila, a kuma so managartan larabawa fiye da managartan sairan mutane. Saboda mafi rinjayan malamai suna ganin larabawa sun fi kowacce al,umma daraja, kuraishawa sun fi dukkan larabawa daraaja.
Kuma Banu hashim sun fi sauran kuraishawa daraj.
.
Akan wannan manyan malamai suke irinsu imam Ahamd kuma haka ingantattu nassosi suka nuna. Kamar hadisan da Manzon Allah (S.A.W ) yace. Hakika Allah ya fifita kuraishawa a cikin ya,yan kainanata, ya fifita Banu hashim a cikin kuraishawa,ya fifita ni a cikin Banu hashim (Muslim...........................)
.
Kuma yace ; ko wadanne mutane akwai tushensu, Kamar yadda zinare da azurfa suke da tushe mafi darajarsu a zamanin jahiliyya su ne mafiya daraja a musulinci in sun fahimc addinin. (Bukhari da
muslim).
.
abiyo mu akashi nagaba
.
DAGA NAKU
ABDULMAJID INB NUHU IBN SULAIMAN


FALALAR SAHABBAI DA GA BAKIN IMAMAI
kashi na biyu
.
CIGABA
.
Abubakar da umar (R.A) sun Kai mutuka wajen girmama Ali(R.A)ta kowacce fuska,
.
Sun fifita shi da sauran banu hashim akan sauran mutane wajen rabon
Dukiyar baitul mali sun gsbatar da shi wajen girmama wa da mutuntawa da kauna da yabo da ba shi matsayin da Allah ya ba shi akan sauran sa,o,insa.
.
Ba a taba jin sun fadi wata mummunar magana ba akansa ko akan wani daga banu hashim.
Sayyadina umar (R.A) yana farawa da iyalan
Manzon Allah (S.A.W) wajen rabon Dukiyar baitul mali.
.
A lokacin sai aka ce ahi zo mu fara sanyen mutane a kundin rabon dukiya sai aka ce shi za mu fara sanya sunanka
.
Sai yace:
.
A'A Ku farad a iyalan manzon Allah (S.A.W)
Shi kuwa Umar ku sa shi inda Allah ya sa shi.
Sai ya fara da banu hashim ya hada su da iyalan Al-muttalib saboda Annabi (S.A.W ) yace:
.
Da ya 'yan hashim da ya'yan muttalib duk abu daya ne ba su rabu da muba a zamanin jahiliyya da zamanin musulunci "
.
(Bukhari, Abu Dawud, masa'i)
.
sai ya farad a Abbas da Ali da Hassan
.
Ya basu fiye da yadda ya baiwa sa'o'insu daga sauran kabilu ya fifita Usamatu Dan zaidu akan dansa(Abdullahi) sai ya yi fushi yace ya zaka fifita Usamah a kai na ?sai yace:
.
Manzon Allah (S.A.W)
.
Ya fi sonsa fiye da babanka.
Wannan abu da muka ambata na fifita banu
Hashim da gabatar da su abu ne sananne a wajen dukkan malaman sira babu wani sabani.
To yanzu wanda yake irin wannan girmamawa ga dangin manzon Allah (S.A.W.) zai yiwu a ce kuma ya zalunci wacce tafi kowa kusanci da shi?, kuma sarauniyar mutan Aljanna, ya kwace mata wani dan abun bai kai ya
Kawo ba, kuma tana cikin damuawar rashin mahaifinta, alhali ya bawa ya'yanta da wadanda suke nesa da shi a kusance ninkin wannan dukiyar?"
..
Ibn Taimiyya ya ci gaba da cewa"
.
Amma shi Ali (R.A) dukkanin Ahlussann suna kaunarsa suna goyon bayansa suna shaidawa cewa yana cikin halifofi shiryayyau, littatafan malaman sunna cike suke da bayanin falalarsa da matsayinsa da kuma zargin masu Zaluntarsa a kowacce kungiya suke, kuma suna yin raddi da gaba da masu zaginsu.
.
Cikin bayanin ingantattun darajojinsa akwai raddi ga mukiyansa
.
(Nawasib) kamar yadda bayanin falalar halifofi uku ke kunshi da raddi ga rafilawa (Makiya sahabba)
.
Duba littafi munhajussunna na ibn Taimiyya juz'i 3 shafuka na, 172'173'134'
.
Da juz'i na 2shafi na 226 da juz'i na 4 shafi na 29 da 30.
.
(Abiyoni a ka shi nagaba)
Mai gabatar wa
Shine Abdulmajid ibn nuhu ibn sulaiman


FALALAR SAHABBAI DA GA BAKIN IMAMAI
(kashi na uku)
.
CIGABA
.
Shi kuwa imamu zahabi (Rahimahullaha)daya daga ciki almajiran ibn Tamiyyah ga abinda yake cewa:
.
Shugabanmu aliyyu yana daga cikin halifofi shiryayyu, muna mutukar kaunars, ba ma da'awa cewa shi må'asumi ne, ko Abubakar. Yan'yansa hasan da husaini jikokin Manzon Allah ne ( S.A.W)
Kuma sune shugabannin samarin Aljanna.
.
Suna cancanci halifanci da Allah ya kaddara hakan.
.
Shi kuma zainal Abidin babban mutum ne yana daga cikin manyan malamai masu aiki da iliminsu.
.
Ya cancan i shugabanci. Ya rayau tare da malamai sa'o'insa wadanda suk fi shi yawan ruwaya da fatawa.
.
Haka dan sa Abu ja' afar Al Bukir shugaba ne masannin fikihu, ya cancanci halifanci. Dan sa ma jaafarus sadik babban mutum ne, malamai, shugaba, ya
Fi
Abu jaafar Al-mansur cancantar zama shugaba.
Dan sa musa Al- kazim yana da daraja da dinbim ilimi yafi harunar Rashid cancantar zama halifa, kuma ya yi rayuwa da wadanda suke sa'o'insa a daraja da daukaka.
Shi ma dansa Aliyyu ibn musa Ar Rida mutum ne mai daraja ga ilimi da bayani mai ratsa zukatau,
Saboda haka ne ma Halifa Ma'amun ya bar wasiyyar in ya mutu ya gaje shi, amma sai ya mutu a shekara ta 203
Hijiriyya.
.
Muhammadul jawad kuwa dansa shi ma shugaban ne mai daraja amma bai kai matsayin iyayensa ba a ilimi da fahimta ba.
Haka dansa wanda ake yi wa lakabi da Al-hadi mai girman, daraja ne da daukaka.
.
Shi ma dansa Al-hassan dan Ali Al-Askari ba a baya yake ba.
Dukkanninsu Allah ya yi musu rahama.
.
Kuma malam zahabi ya ce
Shine sharifi Abul kasim muhammad dan hasan cikon imamai sha biyu wanda SHI'A yan dozing suke cewa wai su ma' asumai ne, babu kuwa wani ma' asumi sai Annabi.
.
Shine wanda suke cewa wai shine wanda ya gaji mahaifinsa, shine Hujja,
Shine Sahibul zaman, Shine wanda ya buya a sirdab a samurra, kuma
Wai yana nan da ransa ba zai mutu ba har sai ya bayyana ya cika duniya da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci.
.
To wannan batu da gaskiya ne ai wallahi Muma dama un so hakan, yanzu dai shekara dari hudu ken an suna jiran bayyanarsa( wato a zamanin zahabi, yanzu kuwa shekara dubu da dari biyu da wan abu ke nan)
.
To kuwa duk wanda ya tura ka wurin wanda ba ya nan ai bai yi maka adalci ba ,to ina ga wanda ya tura gå wanda samsam babu shi.
.
Adalci dai abu ne mai wahala, .
.
Allah ka tsare mud a jahilci da so zuciya"
.
(Duba littafin siyaru A'alam an Nubala juz'i na
13shfi na 120-121)
.
( Abiyomu a kashi nagaba )
.
Mai gabatar wa............:..............................................:.....................


FALALAR SAHABBAI DA GA BAKIN IMAMAI
(4)(kashi na hudu).
.
CIGABA
.
ZAMUTASHI CIKIN MAGANGANUN SAHABBAI DA TABI'AI DA SUKE BAYYANA MATSAYI DA DARAJAR AHLUL BAITI.
.
ALLAH YA YARDA DA SU BAKI DAYA
.
1-Sayyidina Abubakar (R.A) yace
.
"Na rantse da wanda raina yake hannunsa na fi kaunar na kyautata dangin Manzon Allah (S.A.W) fiye da dangi na".
.
( Bukhari 3712 Muslim 1759).
.
2- Sayyadina Umar ( R.A) ya rantse da Allah ga Abbas(R.A) baffan Manzon Allah (S.A.W) yace:
.
''na fi murnar da musuntarka fiye da musuluntar baba na da ya musulunta,saboda Manzon Allah yafi son musulutarka fiye da ta mahaifi na.
.
3-sahabbai (R.A) suna kasance suna girmama Abbas suna shawartarsa kuma bin maganarsa.
.
4-Sayyadina Umar ( R.A) yayi tawasulli da addu'ar Abbas a lokacin da aka yi sallar rokon ruwa.
.
5-Duk lokacin da Sayyidina Umar( R.A) suke hango Abbas yana tafiya a kasa su kuma suna kan abin hawa sai su sauka sai sun wuce shi sannan su hau, saboda girmamawa a gareshi.
.
6-Sayyidina Umar ( R.A) yace Allah ya baiwa Sayyadina Ali daraja uku kowacce daya daga cikinsu ta fiye min jajayen rakuma nune:
.
(1) Auren yar Manzon Allah( s.a.w),
.
(2) Halatta masa zama a masallaci da janaba.
.
(3) Tuta da aka ba shi ranar khaibar.
.
7- Wata rana Abu Hurairah (R.A) yace da Hasan (R.A) nuna wurin da manzon Allah (S.A.W) yake sumbanta a jikinka.
Sai ya kwaye rigarsa sai ya sumbanci cibiyarsa.
.
8-Hasan da Husaini (R.A) sun kasance in dai suna gida mutane sukan yi cincirindo a yi ta turmutsutsu ana ta gaisawa da su.
.
9-Wata rana fatima' yar Ali ( R.A) ta je wurin Umar dan Abdul-Aziz (R.A) a lokac shine gwamnan Mekka, ya girmama ta sosai yace wallahi duk duniya babu iyalan da na fi kauna irinku, na fi son ku fiye da iyalina.
.
10- Sayyidina Umar ( R,A) yayiwa Sayyidina Ali
Tambaya da ya ba shi amsa sai yace ya Allah
kada ka kawo wata matsala sai Ali yana nan.
.
11-Abu Hanifa (R,A) ya kasance yana mutukar girmama Ahlulbaiti yana taimaka musu,yana kuma umarnin dalibansa da yin haka.
Wata rana ya taba bawa wani daga cikinsu wanda ma ba mushahuri ba ne durhami dubu goma sha biyu.
.
12- Imma malik ( R.A) yace Duk wanda ya zagi iyalan
Manzon Allah (S. A.W) a lakada duka a tozarta shi a yanke masa hukuncin dauri mai tsawo har sai ta tuba, saboda ya taba martabar Manzon Allah ( S.A.W).
.
13- imm shafi'i (R.A) yana mutukar girmama a Ahlulbaiti yana bayyana matsayinsu har wasu suka rinka cewa ko ya zama dan Shi,a ne , shi kuwa ya mayar da martani in dai son Ahlulbaiti rafilanci ne to shi ma haka ne .
.
(Duba liltafin Assaw'ikul maharika na ibn hajar Alhaitami shafi na 290-292-da159-160.
.
Wadannan misalai suna karyata maganganun da Rafilawa suke ta maimaitawa na cewa wai Sahabbaai da tabi'a da sauran Alumma suna wulakanta Ahlulbaiti wai suna zaginsu da sauran karerayi mara tushe bare makama.
.
FADAKARWA:
.
Duk wani labari da za ka gani a littatafai da yake
Nuna cin mutunci ko zalunci ga Ahlulbaiti wanda ake dangantawa ga Sahabbai da sauran magabata ba ya wuce dayan abu uku
.
1- Ko dai labarin karya ne.
.
2-Ko akwai gaskiya a. Cikinsa an yi mummunar fassara.
.
3- ko an kara karerayi kan abinda ya inganta.
.
(ZAMU CIGABA)
.
Mai gabar tarwa.......................................................................................................................................................................................


FALALAR SAHABBAI DAGA BAKIN IMAMAI
(kashi na biyar)
.
CIGABA
.
Hakika Allah Ta,ala ya bayyana falalar Sahabbai gaba dayansu babu ragin daka a ayoyi masu yawa a kür'ani, haka kuma Manzon Allah (S.A.W) ya yi a hadisai masu yawa, har ma malamai da dama sun yi littatafai kan haka.
.
A wannan fasali zan kawo kadan daga cikin bayanai da Imamai-jagororin Ahlulbaiti, suka yi dangane da falalar sahabbai da yabo a gare su da girmama su da la'antar masu zaginsu ba kuma tare da ware wani ba daga cikinsu, kuma daga baki har zuci haka suke nufi babu takiyya (munafunci)kumamaganaganun Shi'a in sha Allah.
.
HADISAI DAGA IMAMAI KAN FALALAR SAHABBAI.
.
(1) A cikin tafsirin Aliyyu ibn ibrahim Al-kummi
.
Tafsirul kummi juzi na (1) shafi na 289 yace manzon Allah (s.a.w) ya ambaci Abubakar da sunan"Assidik" inda yake cewa:
.
Daga babansa daga wasu marawaitansa zuwa ga Abu Abdullahi yace:
.
Lokacin da manzon Allah (S.A.W) yake cikin kogo sai yace da abubakar:
.
Yanzu haka ina ganin jaafar shida abokanasa a cikin jirgin ruwa, ina kuma ganin mutanen madina suna zaune a kofar gidajensu.
Sai Abubakar (R.A) ya ce kana ganinsu ya ma 'aikin Allah?
.
Sai ya ce: na'am"sai yace ko zaka nuna min su?
.
Sai ya shafa idanunsa sai yac gansu, sai manzon Allah(S.A.W) yace da shi: kai ne"ASSIDIKU"
.
ZAMU CIGABA
.
Maigaba tarwa .............................................................................................:........:...........................:..............................................:.......


FALALA SAHABBAI DAGA BAKIN IMAMAI
( kashi na shida)
.
(ZAMUCI GABA ) CIKIN HADISAI DAGA BAKI IMAMAI
.
(2) imam Ahasanul Askari Rahimahullah limami na sha daya a wurin Shi'a yan dozin ya ruwaito labarin hijira daga Ali (R.A) ya ce:
Bayan da Manzon Allah (S.A.W) ya umarci Ali(R.A )ya kwana a shimfadarsa sai ya ce da Abubakar Assidik (R.A):
.
Ko za ka yarda ka kasance tare da ni a ranka nemanka kamar yadda ake nema na har a san cewa kai ne kake dafa min kan avonds nake da'awarsa kuma a azabtar da kai a madadi na?
.
Sai Abubakar( r.a)ya ce ya ma'akin Allah da zan rayu iya shekarun duniya ana gana min mafi tsananin azaba,kuma ni ban mutu ba ban rayu ba in dai akan kaunarka ne, to hakan ya fiye min na mallaki komai na duniyar nan ina jin dadinsa,amma in saba maka.
.
Ai da ni da dukiya ta da ya'ya na dukkansu fanasa ne a gareka"
.
Sai manzon Allah (s.a.w) ya ce:
.
Hakika Allah ya Duba zuciyarka ya ga ta yi daidai da maganar bakina ka ya san ya ka zama a matsayin ji da gani da kai da rai a jikina".
.
(Duba Tafsirul hasanul Askari shafi na 164-165)
.
Ma'anar wannan magana ita ce :
.
Kai ni ji na kai ne ga ni na, kai ne ruhi na ! Allahu Akabar.
.
(3) An karbo daga Hasan dan Ali (R.A)(imami na biyu a wurin yan dozin )
Ya ce manzon Allah (S.A.W) ya ce .
.
"Abubakar a matsayin ji na yake,Umar a matsayin gani na yake usman a matsayin zuciya ta yake." Ya ce da gari yaw aye sai na shiga waurinsa na tarar da Amirul muminina a wurinsa da Abubakar da Umar da Usman, sai na ce da shi baba jiya na ji ka fadi wata magana kan wadannana Sahabbaan naka ya maganar ta ke ?
Sai ya nuna su da hannunasa ya ce:
Na'am su ne ji da gani da zuciya".
.
(Duba Tafsirul Burhan: juz'i na 4 shafi na 564-565).
.
In sha Allah zamu cigaba Abiyoni zanci gaba
Mai ga batar wa........................................................................................................................................................................


FALALAR SAHABBAI DAGA BAKIN IMAMAI
(kashi na bakwai)
.
4.A cikin littafin kashful gumma fi maarifatil a imam na irballe juz,i na daya shafi ba 224 ya kawo hadisi da ya kunshi yabon Ansat inda yace"MANZON ALLAH SAW YACE
.
" YA ALLAH. ka gafartawa ansat (mutanen madinah) da iyayen ansat da jikokin ansat ,ya ku jama'ar ansat ba zaku yarda ace mutane si kima gidajinsu da awaki da rakuma ku kuma ku kima da MANZAN ALLAH SAW?
.
5..An tambayi lmam rida Aliyu bin Musa shin hadisin da Manzon ALLAH SAW yace "sahabbaina kamar taurari ne duk wanda kuka yi koti da shi a cikinsu zaku shiriya shin wannan hadisin ya inganta? Sai yace" ya inganta."
.
Duba littafin Irin Akhbar Arrida na Kummi 2/87.
.
6.An karbo daga Musal Kazim R.a yace Manzon ALLAH SAW Yace"Ni aminci ne (garkuwa) ga sahabbai na,idan aka karbo raina abin da aka alkawaranta sahabbai na(fitintinu) sai ya kusanto ,kuma sahabbai na aminci (garkuwa) ga Al' ummata , idan sahabbai na suka kauce sai abinda aka Alkawartawa al' ummata ya zo musu, kuma wannan addinin zai kasance sama da dukkanin addininai matukar a cikinku akwai wadanda suka ganni (sahabbai).
.
Duba Bisharul Anwar na Majlisi Juz'i na 22 shafi na 309-310.
.
7.Kuma dai a cikin Bisharul Anwar din (22/305) an rawaito daga Abu Anas yace
.
" Manzon ALLAH SAW ya ce
.
" Aljanna ta tabbata ga duk wanda ya ganin ya yi imani da ni,Aljanna ta tabbata ga wanda ya ga wanda ya ganin".
.
Bayan Wadannan bayanai yanzu ga salla- salla daga Imam yadda suka bayyana falalar da matsayin Sahabbai R.A.
.
ZAMUCI GABA IN SHA ALLAH.


FALALAR SAHABBAI DAGA BAKIN IMAMAI
[kashi na takwas]
.
[1] IMAM ALI [R.A];
An tanbayi Sayyidina ali [R.A ] me yasa musulmi suka zabi abubakar ya zama halifan ANNABI?
sai yace hakika mun san yafi kowa cancatar wannan matsayin. shine wanda ya kasance tare da manzon ALLAH [S.A.W] lokacin da ya fake a cikin kogo hakika mun san nagartarsa . kuma shine wanda manzon ALLAH [S.A.W] ya umarce shi yayi limanci tunda ranasa.
.
[ sharhu nahjul balaga na ibn abil hadid"1/332.
.
Har,ila yau imami ALI [R.A] yace ba don mun tarbbatar da cancantar ABUBAKAR ga halifanci ba dab amu kyale shi ya yi ba
.
[ sharh nahjul balaga 1/130.].
.
Kuma ya yabi ABUBAKAR DA UMAR inda yake cewa:
.
''KUMA wanda ya fi su [SAHABBAI] falala da nasiha ga ALLAH da manzonsa sune halifa SADIDIK DA HALIFA FARUK , na rantse da ALLAH suna da babban ma tsayi a musulunci kuma rashinsu babbar asara ce ga musulunci. ALLA ya yi musu rahama ya saka musu da alheri.
.
[ sharhin nahjul balaga na misam 1/31].
.
ZAMUCI GABA INSHA ALLAH MAI GABATARWA ...:.........................................


FALALAR SAHABBAI DAGA BAKIN IMAMAI
( kashi na tara)
.
Wata rana ciwon kwibi kwiba ya kama sayyadina ABUBAKAR sai sayyadina ALI yazo da kansa yana yi masa sakiya:
.
( Arriyadun nadira na muhibbut tabari juz`I (1).
.
A wata huduba da yayi saboda an gaya masa cewa wadansu mutane suna zagin ABUBAKAR DA UMAR yace:
.
Mene ne dalilin da yasa wadansu mutane suka taba mutuncin yan uwan manzon ALLAH (S.A.W).
WAZIRINSA abokinsa shugabannin kuraishawa ubannin musulmai (ABUBAKAR DA UMAR )?
.
Babu ruwa na da abin dasuke fada kuma sai na hukunta masu yin hakan sun yi rayuwa kauna da amana da taimakon addini da manzon ALLAH (S.A.W).
.
AZAMANINSA suna umarni da kyakkyawa suna hani ga mummuna suna fushi saboda ALLAH suna hukunta masu saba masa . annabi (S.A.W) YANA daukar shawararsu fiye da kowa yana kaunar fiye dakowa saboda gaskiya rsu da ya gani akan al amarin ALLAH ya bar duniya yana mai yarda da su .
.
Kuma dukkanin musulmi suna masu yarda da su ba su taba sabawa koyarwa manzon ALLAH (S.A.W) ba a lokacin da yake da rai da bayan wafatinsa har suka mutu ALLAH ya jikansu na rantse da wanda yake fitar da kwaya yake halittar rai ba mai kaunarsu sai muminai mai falala, bai mai kinsu sai dan wuta mai barin addini kunarsu ibada ne.kinsu barin addini ne a wata ruwayar sai ya ce :.
ALLAH ka la anci masu kinsu. Duba littafin taukul hamama daga littafin izhabu fi antumar rafida. 242-245.
.
Ya Dan uwa masoyin imam ALI ka yi lura da wannan magana ka yi hattara in kana cikin makiyansu ka yi maza ka tiba. Ya ALLAH ka shirye mu gaba daya
.
ZAMUCI GABA IN SHA ALLAH MAI GABATARWA:...................................


FALALAR SAHABBAI DAGA. BAKIN IMAMAI
[ KASHI NA GOMA]
.
Zamucigaba
Kamar yarda imam ALI [R.A] ya yabi sayyadina USMAN [R.A] dacewa babu wani abu dana sani wanda kai ba ka san shi ba kuma zan shiryar da kai ga abinda ba ka saniba ba mu gabace ka da wani abu ba ballantana mu baka labari kuma bamu kebanta da sanin wani abu ba ballantana mu isar maka da shi .
.
Hakika kaga abinda muka gani ka ji abinda muka ji, ka zauna da manzon ALLAH [S,A,W] kamar yadda muka zauna da shi kuma ABUBAKAR DA UMAR basu fi ka cancantar aiwatar da gaskiya ba kuma kai ka fisu kusanci na jini da annabi kuma kasami surukuntar da ba su samuba
.
“[NAHJUL BALAGA 2/357].
.
An karbo daga imam Assadik daga magabatansa da ga ALI ya ce .
.’’ ina yi mukub wasiyya da SAHABBAIN annabinku , kada ku zage su suna wadanda ba sa kirkiri komai ba a bayansa [bidi,a] kuma a ba su goyan masu kirkira ba, saboda manzon ALLAH [S,AW] YA YI wasiccin alheri a gare su
.
“[BIHARUL ANWAR 22/305/306].
.
Kai har wadanda suka yakeshi a yakin siffin imam ALI [R.A] ya hana a zage su ko a kafirta su.
.
GA ABINDA YAKE FADA GA MASOYA BAYANSA.
.
ABIYOMU AKASHI NAGABA IN SHA ALLAH ……………………………………………………………………………………………………………………………………………………………………………………………………


FALALAR SAHABBAI DAGA BAKIN IMAM
[KASHI NA GOMA SHA DAYA 11]
.
yanzu zamu ci gaba daga inda muka tsaya insha ALLAHU.
Kai har wadanda suka yake shi a yakin SIFFIN,IMAM ALI R.A ya hana a zage su ko a kafirta su.Ga abinda yake fada ga magoya bayansa.
.
"NI bana kaunar ku kasance masu zage-zage,ai in kuka fadin halinsu a ayyukansu ma ya wadatar,kuma a maimakon ku yi ta zaginsu kamata ya yi ku dinga addu'ah ku na ce
.
"YA ALLAH ka tsare jininmu da nasu,ka shirye tsakaninmu da su,ka shirye su daga batan da suke ciki,har kowa ya fahimci gaskiya,masu tawaye su daina
.
."(nahjul balaga 2/469.)
.
AN Karbo daga ja'afarus sadhk ya karbo babansa ya ce"hakika Ali ya gayawa magoya bayansa cewa
.
"Mu fa ba muna yakar su ba ne don muna ganin su kafirai ne ba,haka su ma ba su na yakar mu bane saboda su na ganin mu kafirai ne ba,sai da fahimtar mu ce ta banbanta,su suna ganin akan gaskiya suke,mu ma muna ganin akan gaskiya.
.
"[KURbuL Isnad na Himijar daga Izhabu fa antamur rafida 246-247].
.
Har'ila yau Shehu imam sadik ya rawaito daga mahaifinsa cewa
.
"SAYYADINA ALI R.A bai ta6a kafirta ya yake shi ba,bai kuma ce su munafukai ba ne,sai dai a koda ya yaushe yana cewa
.
"yan uwanmu ne suka yi mana tawaye"
.
.[wasi'ilus shi'a 15/83].
.
To ai masu kafirta Sahabbai r.a da dukkanin musulmin da ba sa bin ra'ayinsa kuma suna da'awar kaunar da bin Imamu Ali?
.
To kun ji dai har wadanda suka yi masa tawaye suka yake shi baya kafirtasu,baya zaginsu,cewa ma yake"yan'uwansane",to kai da wa kake koyi?
.
To yan'uwa ayi hattara.
.
Ku biyo ni a darasi na gaba don jin maganar IMAM HASSAN R.A.
Mai gabatarwa. . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . .


FALALAR SAHABBAI DAGA BAKIN IMAMAI
[KASHI NA GOMA SHA BIYU] (12)
.
IMAM HASSAN R.A
Masu hikima sun ce"kyan da ya gaji ubansa",hakika 'ya'ya da jikokin sayyidina Ali r.a sun haifu ta yadda suka dauko halinsa da halin kakansa MANZON ALLAH S.A.W su na kaunar sahabbai r.a su na girmama su,su na yabonsu kamar yadda kakansa S.A.W da babansa suka kasance suna yi. Abin haka yake,ai barewa ba tayi gudu ba,danta ya yi rarrafe.
.
IMAM HASSAN R.A Shi ne babban dan sayyidina ALI R.A ya kasance yana matukar girmama ABUBAKAR DA UMAR R.A Wannan ne yasa lokacin da zai sauka daga halifancinsa ya bar wa MU'AWIYYA R.A domin a zauna lafiya ,ya kafawa MU'AWIYYA sharadi cewar
.
"zai yi aiki da qur'ani da sunnar MANZON ALLAH S.A.W zai kuma bi tafarkin halifofinsa shiryayyu [ABUBAKAR,UMAR,USMAN,ALI R.A].
.
{muntahul aamal 2/212 daga asshi'a wa ahlul baiti 56}.
.
An kar6o daga zaid ibn wahab aljuharu ya ce
.
"lokacin da aka soki Hassan r.a dan Ali r.a a mada'in sai na zo wurinsa yana jiki ,sai na ce dan 'yar MANZON ALLAH S.A.W me ka ke gani,domin mutane sun shiga dimuwa?,sai ya ce
.
"wallahi ni ina ganin Mu'awiyya r.a yafi min wadannan mutanen,su na cewa wai su magoya bayana ne. ['yan shi'a] amma gashi neman kashe ni suke yi,su wawashe min kayana ,su kwashe dukiyata,wallahi da na bari su kashe ni da iyali na,su tozarta gara na yi sulhu da Mu'awiyya r.a na tsare jini na sami aminci da iyalaina
.
"[AL-IHTIJAJ 2/69}.
.
A biyo ni a darasi na gaba,domin jin maganar IMAM ZAINUL ABIDIN R.A,INSha ALLAHU.
Mai gabatarwa. . . . . . . . . . . . , , . . . . . . . . . . . . . . . . . . . .


FALALAR_SAHABBAI_DAGA_BAKIN_IMAMAI.
{KASHI NA GOMA SHA UKU 13}.
.
IMAM ZAINUL ABIDIN R.A
A Cikin addu'o'insa da aka tattara imam ZAINU ABIDIN R.a yana addu'ah ga sahabban ANNABI S.A.W yana kuma yabansu yana cewa
.
"ya ALLAH ka yi rahama ta musamman ga sahabban MUHAMMADU S.A.W wadanda suka yi kyakyawan zama da shi,suka goyi bayansa,suka yi gaggawa zuwa wurinsa,suka yi tsere wajen amsa hujjar manzancinsa,suka rabu da matansu da yayansu domin daukaka addininsa,suka yaki iyayensu da yayansu domin tabbatar da annabtarsa,kumasuka samu nasara saboda shi"
.
[ASSAHIFATUS SAJJADIYA DARUL BALAGA BUGU NA biyu 2].
.
An karbo daga yahya dan abi kasir daga ja'afar dan Muhammad daga babansa[a.s]ya ce
.
"wani mutum ya je wurin babana ZAINUL ABIDIN A.S sai ya ce me za ka fada game da ABUBAKAR R.A? SAI YA CE "KAI ! Ma kana ce masa SADDIKU?,Sai ya ce"tir da kai ai wadanda suka fi ni ma su na ce masa assadik shine MANZON ALLAH S.A.W da muhajirun da ansar,duk wanda bai kira shi da saddik ba,kada ALLAH ya gasgata maganarsa.kai ka so ABUBAKAR DA UMAR,ka goyi bayansu[ka mika wilayarka gare su] in ma hakan laifi ne to na dauke maka.
.
"{kashful gumma daga izhabu fa antumur rafida 241}.
.
A karshe da fatan zaku biyo ni domin jin maganar IMAM MUHAMMAD IBN ALI ALBAKIR R.A,a darasi na gaba INSHA'ALLAHU.
Mai gabatarwa. . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . .


FALALAR SAHABBAI DAGA BAKIN IMAMAI.
{kashi na goma sha hudu 14}.
.
IMAM MUHAMMAD IBN ALI ALBAKIR R.A
Ya dan uwa masoyin AHLUL BAITI da sahabbai r.a saurari yadda kogin ilimi Muhammad Bakir yake kwarara yabo kan SAYYIDINA ABUBAKAR R.A da wanke shi daga sharrin da ake yi masa na cewa wai wai wai ya zulunci Ahlul Baiti.
.
An karbo daga Urwata dan Abdullahi ya ce"na tambayi ABU JA'AFAR MUHAMMAD dan Ali [albakar]kan hukuncin da yi wa takkuba ado."sai ya ce babu laifi,saboda ABUBAKAR ASSADIK R.A ya yi wa takkwabinsa ado,sai na ce kai ma saddik din kake ce masa? Sai ya yi zumbur ya mike ya fuskanci alkibla yana cewa "ASSADIK ! Assadik !! Assadik !!! Kuma duk wanda bai kira shi da Assadik ba,kada ALLAH ya gasgata maganarsa a duniya da lahira"
.
[kashfulgumma 2/360].
.
Kuma ya tabbata daga muhammadul bakar da zaid ibn Ali sun ce
"kurunkus"
da take tabbatar da karyar duk wani labari da yake nuna zulunci ko danniya ko kwace ga AHLUL BAITI,da ake cewa sahabbai r.a sun yi har ake daukar alhakinsu ake gaba da su ana ta la'antarsu da sunan kaunar ahalul baiti,to su dai da ake cewa wai don su ake yi ga matsayinsu nan karara.ALLAH ka ganar da mu baki daya,amin.
.
Yanzu sai ku biyo ni mu gangara taskar mai tsarki dan tsarkaka IMAM JA'AFARUS SADIK R.A
.
Amma kash ! Sai ku biyo ni a da darasi na gaba,INSHA'ALLAHU.
Mai gabatarwa . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . . .


FALALAR SAHABBAI DAGA BAKIN IMAMAI
{KASHI NA GOMA SHA BIYAR 15}.
.
IMAM JA'AFAR ASSADIK R.A
An karbo daga abu basir ya ce wata rana ina zaune a wurin Abu Abdullahi Ja'afurus Sadik,sai Ummu Khalid ta shiga tana neman izini,sai Abu Abdullahi ya ce"
.
''ko kana so ka ji zancenta", sai nace "i",sai ya bata izini ta shigo,ya zaunar da ni kan shimfida, sannanta shigo,ta yi magana.SAI NA fahimci mace ce mai fasaha,sai ta yi masa tambaya akan ABUBAKAR DA UMAR,sai ya ce ki so su, ki yi musu biyayya.Sai ta ce to ka yarda in na je lahira na ce kai ne ka umarce ni da na so su?, sai ya ce i.
.
{RAUDATUL KAFI 88}.
.
An karbo daga ja'afurus sadik ya ce"
.
''ABUBAKAR R.A babana ne ta fuska biyu 2"saboda babarsa ita ce Ummu Farwah yar Alkasim dan Muhammad dan Abubakar ,ita kuma babarta [wato Ummu Farwah, ita ce Asma'u 'yar Abdurrahman dan Abubakar Assadik.
.
[kashfuk gumma 2/161].
.
Wani mutum ya tambayi Imam Assadik R.A ya ce dan MANZON ALLAH me zaka fada kan ABUBAKAR DA UMAR R.A? Sai ya ce
.
"su shugabanni ne adalai sun kasance akan gaskiya 'sun mutu akanta. ALLAH ya yi musu rahama ranar kiyama.
.
[IHKAFULHAK NA SHUSHATAR 1/161].
.
Imamus SADIK R.A yana cewa sahabban MANZON ALLAH s.aw su dubu goma sha biyu 12,000 ne,DUBU TAKWAS 8,000 MUTANEN MAdina ne,DUBU BIYU 2,000 MUTANEN MAKkah Ne,Dubu biyu 2,000 wadanda suka musulunta bayan an ci makka da yaki,duk cikinsu babu mai akidar akadiriyyah,ko murji'a,ko kawarij,ko mu'utazila,ko mai bin ra'ayinsu,sun kasance su na kuka dare da rana saboda tsoron ALLAH,su na cewa ALLAh Ka karbi rayukanmu tun kafin duniya ta baude mana
.
"[biharul anwar al khisat 64].
.
IMAMA ALHANAUL ASKARI R.A shine wanda aka ce shine mahaifin mahadi,iman na sha biyu 12 a wurin yan shi'a.Ga abinda da yake fada a cikin tafsirinsa:-
.
"1.Hakika Annabi Musa A.s ya tambayi Ubangiji S.WT,Shin akwai akwai sahabban da suka fi nawa daraja? ,sai ALLAH [SWT] YA CE
.
"YA MUSA BAKA SAN CEWA SAHABBAN MUHAMMADU AKAN SAHABBAN ANNABAWA,KAMAR FIFIKON MUHAMMADU NE,AKAN DUKKAN ANNABAWA DA MANZANNI BA?
.
"[TAFSIRUL HASANUL ASKARI 65].
.
2. Ya yi bayani akan irin azabar da za'a yiwa makiya sahabbai da Ahlul baiti ya ce
.
"za'a yi makiya sahabbai da AHLUL BAITI azabar da za a rabawa dukkanin halittu sai ta halakar da su baki dayansu
.
"[tafsirul askari 196].
.
ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH YA DAN'UWA mai neman gaskiya mai kaunar Ahalul baiti da sahabban MANZON ALLAH S.AW anan zan dan dakata da wannan aiki zuwa wani dan lokaci,ina rokon ALLAH ya cika zukatanmu da kaunar da koyi da wadannan bayin ALLAH,ALLAH kuma ya tsare mu da gaba da su da dukkan wani musulmi,ALLAH ya watsa aniyar masu rarraba kan musulmai,ameen.
.
A karshe,ina fatan wadannan takaitattun bayanai masu amfani za su gamsar da kai don fahimtar gaskiya kan matsayin sahabbai R.A a wurin AHLUL BAITI,ALLAH ya yarda da su baki daya.
.
NA GODE,a bisa bibiya ta da ku ka yi don jin wannan maudu'i mai amfani,sai mun hadu a gaba,INSHA'ALLAHU a wani maudu'in na daban.
.
NAKU,DAN'UWANKUA MUSULUNCI.
Abdulmajid ibn Nuhu.


Koma Saman Shafi



Kuna iya tuntu6ar mu ta wadannan hanyoyin
Abdul-majid Ibn Nuh ta face book

KO TA SHAFIN MU NA FALALAR SAHABBAI DAGA BAKIN IMAMAI TA FACE BOOK.

Ko ta watsAp A 07063276717
Bugo mana waya ta nan
Bugo mana waya ta nan
Bugo mana waya ta nan
Ko ta Email A

Home


Copyright © 2014 - 2015By:- Abul-majid Ibn Nuoh Powered by- Basheer journalist sharfadi